Home Labaru Sanata Orji Kalu Na Shirin Shiga Tseren Neman Kujerar Shugaban Kasa

Sanata Orji Kalu Na Shirin Shiga Tseren Neman Kujerar Shugaban Kasa

84
0

Shugaban Kwamitin ladaftarwa na majalisar dattawa Sanata Orji Kalu, ya ce zai duba yiwuwar tsayawa takarar shugaban kasa idan har jam’iyyar APC ta mika tikin kujerar shugaban kasa ga yankin kudu maso gabas.

Sanatan ya bayyana haka ne, a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke.

Wata majiya ta ce, tuni kungiyoyi da dama sun lamunce wa Sanata Kalu kuma sun nuna shirin su na son ganin ya zama dan takarar jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa na shekara ta 2023.

Yayin da ya ke nuna godiya ga kungiyoyin da ke goyon bayan takarar sa, Sanatan ya ce kungiyoyin sun ga cewa ya cancanci zama shugaban Nijeriya, sai dai ya ce har yanzu bai gama yanke shawarar tsayawa takarar ba.

Leave a Reply