Home Labaru Na Ranste Da Al-qur’ani Ba Zan Nemi Tazarce Ba – Buhari

Na Ranste Da Al-qur’ani Ba Zan Nemi Tazarce Ba – Buhari

10
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi rantsuwa da Al-Qur’ani mai girma cewa wa’adinsa na karewa ba zai nemi yin tazarce a kan kujerar mulki ba.

Buhari ya bayyana haka ne, yayin wata ganawa da ya yi da wasu ‘yan Nijeriya mazauna Kasar Saudiyya, a lokacin da ya ke shirin bankwana da kasar.

Mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce shugaba Buhari ya bada tabbacin cewa wa’adin sa na karewa zai sauka daga kujerar mulki.

Shugaba Buhari, ya rantse da Al-Qur’ani mai tsarki cewa zai yi mulki kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, kuma da zarar wa’adin mulkin say a kara babu zancen Ta-Zarce, don haka ba zai yarda da hakan ba.

Ya ce a cikin watanni 18 da su ka rage na wa’adin mulkin sa, zai yi duk abin da zai iya yi na inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.