Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya CAN, ta gargadi jam’iyyun siyasa da cewa kada su yi kuskuren zaben Musulmi da Musulmi a matsayin ‘yan takarar Shugaban kasa da mataimaki a shekara ta 2023.
Sakataren kungiyar na kasa Joseph Bade Daramola ya bayyana haka a Abuja, inda ya ce yin hakan ya na da hadari ga zaman lafiya da hadin kan ‘yan N’jeriya.
Ya ce kungiyar CAN ta na bukatar yin daidaito tsakanin addinai biyu wajen zaben abokan tafiyar yan takarar kujerar shugaban kasa, don haka ba su yarda Musulmi da Musulmi ko Kirista da Kirista ba.
Joseph Bade, ya ce duk jam’iyyar da ta yi kokarin yin haka za ta sha kashi, domin yanzu ba shekara ta 1993 ba ce, kuma ko yanzu da Musulmi da Kirista ke mulki amma Kiristoci su na shan bakar wahala.
Sakataren ya kara da cewa gargadi su ke yi, kuma za su dauki mataki idan ba a dauki gargadin su ba, sannan ya yi kira ga Tinubu ya dauki mataimaki daga yankin Arewa, Atiku Abubakar ya dauki Kirista daga yankin kudu.