Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Ondo, ta musanta rahotannin da ke cewa ta kama maharan da su ka kashe masu ibada sama da 40 a harin da su ka kai kan Cocin Katolika na St. Francis a jihar.
Rahotannin da aka rika yaɗawa a shafukan sada zumunta dai sun bayyana cewa, dakarun haɗin gwiwa na sojoji da ‘yan sanda da na rundunar Amotekun ne su ka kama maharani.
Haka kuma, rahotannin sun yi iƙirarin cewa, an kai mutanen fadar Mai Martaba Olowo na Owo Oba Ajibade Ogunoye, inda mutane su ka yi tururuwa domin ganin waɗanda ake zargin.
Sai dai basaraken ya musanta lamarin da cewa rahoton ba gaskiya ba ne, kuma Mutane sun yi ta zuwa fada domin ganin su amma Olowo ya sahida masu babu wanda aka kai fadar.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Ondo Funmilayo Odunlami, ta ce babu wanda aka kama da zargin kai harin na ranar Lahadi da ta gabata.














































