Home Labaru Ilimi Yajin Aiki: Kotu Ta Ce Kwamitin Da Gwamnatin Kaduna Ta Kafa Haramtacce...

Yajin Aiki: Kotu Ta Ce Kwamitin Da Gwamnatin Kaduna Ta Kafa Haramtacce Ne

57
0

Kotun Sauraren Ƙararrakin Biyan Haƙƙin Ma’aikata, ta ce Kwamitin Bincike da Gwamnatin jihar Kaduna ta kafa a kan Ƙungiyar ‘Yan Ƙwadago ta jihar haramtacce ne.

Mai Shari’a Obaseki, ya ce Gwamna El-Rufa’i ba ya da ikon kafa wa ‘yan ƙwadagon jihar kwamitin binciken yajin aikin su na ranar 16 zuwa 19 Ga watan Mayu na shekara ta 2021, da kuma binciken duk abin da ya biyo bayan yajin aikin.

Kotun ta ce, tabbas Gwamna zai iya kafa Kwamitin Bincike, amma ba ya da ikon kafa kwamitin binciken ayyuka ko rikicin ƙungiyar ƙwadago, kuma abubuwan da gwamnati ta bukaci kwamitin ya bincika sun danne haƙƙin da dokar ƙasa ta ba ma’aikatan ƙwadago, saboda haka kwamitin haramtacce ne ba ya da ikon yin wani bincike.

Ta ce Gwamna El-Rufa’i ya yi tuwo na mai na, domin shi ya kafa kwamitin kuma shi ya naɗa ‘yan kwamitin, sannan ya umarce su da cewa shi za su kai wa sakamakon binciken, lamarin da kotun ta ce ya nuna shi ne kuma zai hukunta su.

Tuni dai kotun ta haramta wa Gwamna El-Rufa’i sake kafa wani kwamitin bayan wanda ta ruguza, sannan a karshe ta ci Gwamnatin Jihar Kaduna tarar Naira dubu 500, waɗanda ta ce a biya ƙungiyar ƙwadago, wadda ita ce ta shigar da kara.