Hukumar Yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta kai karar tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido da dan sa Mustapha Lamido a kotun koli.
An dai gurfanar da tsohon gwamnan ne tare da ‘ya’yan sa biyu Aminu da Mustapha da Aminu Wada Abubakar da kamfanonin su na Bamaina Holdings da Speeds International a gaban mai shari’a Ijeoma Ojukwu na babbar kotun tarayya da ke Abuja, bisa tuhume-tuhume 37 na halasta kudaden haram da ya kai Naira biliyan 1 da miliyan 35.
An zargi Sule Lamido da cin zarafi a matsayin sa na gwamna tsakanin shekara ta 2007 zuwa 2015, tare da karkatar da wasu makudan kudade da ya karba daga kamfanonin da gwamnatin jihar Jigawa ta ba shi kwangila a karkashin sa.
Shari’ar da ta fara a shekara ta 2015, hukumar ta kira shaidu sama da 16 kafin ta rufe karar ta, sai dai mai shari’a Ojukwu ya yi watsi da lamarin, ya kuma amince da maganar da EFCC ta gabatar cewa Sule Lamido da sauran wadanda ake kara su kare kan su. A cikin sanarwar daukaka kara da aka shigar a kotun koli, hukumar EFCC ta na neman kotun ta yi watsi da dukkan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke tare da bada umarnin a maida karar zuwa kotun koli.