Rundunar sojin Nijeriya, ta ce ta na jiran umurnin kungiyar ECOWAS ne kawai domin zuwa Jamhuriyar Nijar.
Wannan dai ya biyo bayan matsayar da kungiyar ECOWAS ta cimmawa ne cewa za ta dauki matakin soji idan har dakarun da su ka yi juyin mulki a Nijar ba su maida kasar a kan turbar dimokradiyya ba.
Tun farko dai shugaban hukumar gudanarwa ta kungiyar Mousa Traore, ya fada a birnin Abuja jim kadan bayan taron shugabannin kasashen yankin cewa har yanzu a hukumance Mohamed Bazoum ne Shugaban kasar Nijar.
Don haka ya ce dole ne a cikin mako daya a koma tsarin mulki ko a yi amfani da karfin soji a maida Shugaba Bazoum a kan karagar mulki
Mousa Traore, ya ce tuni har an umarci manyan hafsoshin rundunonin tsaron kasashen yankin su gana domin shirin tunkarar sojojin da su ka yi juyin mulkin.
Babban hafsan hafsoshin rundunar tsaron Nijeriya Janaral CG Musa, ya ce a bangaren su a shirye su ke domin tunkarar masu juyin mulki a Nijar, da kuma dawo da zababbiyar gwamnatin farar hula da jama’a su ka zaba.