Home Home Majalisar Wakilai Ta Yi Kira Da A Sasanta Kan Zanga-Zangar Cire Tallafin...

Majalisar Wakilai Ta Yi Kira Da A Sasanta Kan Zanga-Zangar Cire Tallafin Mai

122
0

Majalisar wakilai ta yi kira ga kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, da sauran kungiyoyin da su ka yi hadaka su dakatar da zanga-zangar lumana da su ke gudanarwa a fadin Nijeriya game da cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.

Kiran Majalisar dai ya na kunshe ne a cikin wata sanarwar da mai magana da yawun majalisar Akin Rotimi ya fitar, inda ya ce  maimakon shiga zanga-zangar, abin da ya fi dacewa shi ne a hau teburin sulhu, wanda hakan ne babbar mafita ga ma’aikatan Nijeriya ba tare da jefa rayuwar ‘yan Nijeriya cikin mawuyacin hali ba.

Ya ce duk da rokon da gwamnatin tarayya ta yi wa NLC na ta dakatar da shiga zanga-zangar, amma a matsayin su na shuwagabannin jama’a su na tausaya wa ‘yan Nijeriya a kan halin kuncin da cire tallafin man ya jefa su.

Akin Rotimi, ya ce su na sane da cewa NLC ta na da ‘yancin gudanar da zanga-zangar lumana, domin sama wa ma’aikata da ‘yan Nijeriya saukin rayuwa a kan kalubalen da kasar nan ke ciki a yanzu.

Leave a Reply