Home Labaru Harin Ekweramadu: Najeriya Na Farautar ‘Yan IPOB A Jamus

Harin Ekweramadu: Najeriya Na Farautar ‘Yan IPOB A Jamus

460
0

Jakadan Najeriya a Jamus Yusuf Tugga, ya ce za su tabbatar cewa an kama tare da hukunta wadanda suka ci mutuncin Sanata Ike Ekweremadu a lokacin wani taro na ‘yan kabilar Igbo a Jamus.

Yusuf Tugga, ya ce ofishin jakadancin Najeriya a Jamus na iya  bakin kokarin sa wajen ganin an hukunta wanda suka yi wannan rashin mutunci.

Sai dai ya koka a kan cewa ba a sanar masu da zuwan tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan ba, abin da ya sa ba su yi masa wani tanadi ba kenan.

Jakadan na Najeriyan a Jamus, wanda ya halarci wurin taron jim kadan bayan afkuwar lamarin, ya ce da an sanar da zuwan  Ekweremadu, Jamus a hukumance da babu yadda za a yi wannan abu ya faru da shi.

Ya kara da cewa sun bayyana wa kasar Jamus ceaw lallai-lallai ya kamata ta haramta ayyukan kungiyar ta IPOB a Jamus kamar yadda gwamnatin Najeriya ta haramta.

Yusuf Tugga, ya ce ya tabbata Jamus za ta kula da abin da suka dade suna fada mata a kan kungiyar IPOB cewa ‘yan ta’adda ne kuma akwai ‘ya’yan ta a kasar su da ya kamata ta dau matakai a kan su.