Home Labarai Badaƙalar Filaye: Hukumar Shari’a Ta Dakatar Da Ma’aikatan Kotu A Kano

Badaƙalar Filaye: Hukumar Shari’a Ta Dakatar Da Ma’aikatan Kotu A Kano

39
0
Court and Law.webp
Court and Law.webp

Hukumar Shari’a ta jihar Kano (JSC) ta ladabtar da wasu Magatakardan Kotun Musulunci biyu kan badaƙalar filaye.

Kakakin Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim ya sanar cewa ɗaukar matakin ya zo ne a yayin taron hukumar karo na 75 da aka gudanar a ranar 12 ga watan Satumbar nan da muke ciki.

Ya ce hakan na zuwa ne bayan kwamitin bincike da aka kafa kan ƙorafin da aka yi a kan su ya miƙa rahoton sa.

Binciken ya gano cewa Jamilu Ibrahim tare da waɗanda suka haɗa baki sun karɓi kuɗaɗe ba bisa ka’ida ba, suka bayar da takardar mallakar fili ta hanyar yaudara, domin sayar da wasu filaye guda biyu.

Binciken ya ce hakan ne ya sa kwamitin ya ba da shawarar a kori Jamilu Ibrahim daga aiki, amma hukumar shari’a ta dakatar da shi ba tare da biyan albashi ba har sai an kammala shari’ar da yake fuskanta a gaban kotun Majistare.

Shi kuma Zubairu Sulaiman, wanda magatakardan Babbar Kotun Musulunci ne, an same shi da karɓar Naira miliyan ɗaya ta asusun sa na ƙashin kan sa a matsayin la’ada bayan siyar da filayen guda biyu,

inda aka dakatar da shi na tsawon wata huɗu ba tare da biyan albashi ba, kamar yadda kwamitin binciken ya bayar da shawara.

Leave a Reply