Home Labaru A Shirye Nake In Fuskanci Osinbajo A Kotu – Timi Frank

A Shirye Nake In Fuskanci Osinbajo A Kotu – Timi Frank

380
0
A Shirye Nake In Fuskanci Osinbajo A Kotu - Timi Frank
A Shirye Nake In Fuskanci Osinbajo A Kotu - Timi Frank

Mai rajin kare hakkin bil Adama Kwamred Timi Frank, ya ce a shirye ya ke ya fuskanci mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a gaban kotu, game da zarge-zargen cewa Osinbajo na da hannu a badakalar naira biliyan 90.

Karanta Wannan: Taron Ilimi: Farfesa Yemi Osinbajo Osinbajo Ya Ziyarci Jihar Kano

Yayin wata zantawa da ya yi a gidan talabijin na Channels, Mista Frank ya ce ya na nan a kan bakan sa cewa Farfesa Osinbajo na hannu badakalar.

Idan dai za a iya tunawa, a baya Timi Frank ya bukaci hukumar (EFCC, Daraktan hukumar tsaro ta DSS, da hukumar ICPC su yi bincike a kan ikirarin da ya yi, cewa mataimakin shugaban kasa ya karbi kudaden da ake magana a kai daga hannun hukumar tattara kudaden shiga domin daukar nauyin zaben shugaban kasa da ya gabata.

Frank, ya kuma kalubalanci Farfesa Osinbajo ya kai karar shi kotu a kan zargin, kalubalen da mataimakin shugaban kasa ya dauka ba da wasa ba.

Yayin da yake maida martani a kan zargin, Osinbajo ya bayyana ce a shirye ya ke ya ajiye kariyar da kundin tsarin mulki ya ba shi domin wanke kan sa daga zargin.