Home Labaru Babban Limamin Masallacin Ka’aba Sheikh Sudais Ya Ƙaddamar Da Na’urar Feshin Magani

Babban Limamin Masallacin Ka’aba Sheikh Sudais Ya Ƙaddamar Da Na’urar Feshin Magani

10
0

Shugaban manyan masallatai biyu mafiya daraja dake kasar Saudiyya Sheikh Abdulrahman Al-Sudais ya ƙaddamar da wata na’ura mai feshin maganin kashe ƙwayoyin cuta a Masallacin Ka’aba.

Sudais ya ƙaddamar da na’urar ce a ranar Laraba inda za ta rika aiki na tsawon sa’o’I huɗu sannan tana iya ɗaukar lita 68 na ruwa, ta kuma yi zagaye na murabba’in kilomita 2,000 a cikin sa’a guda.

Sheikh Sudais ya jaddada cewa ofishinsa na aiki da bayanan da yake samu domin tsara yadda abubuwa za su ringa gudana a Masallatan Makkah da Madina domin bin dokokin ƙasa da ƙasa tareda tabbabar da cewa mahajjata sun ji daɗin ziyararsu a masallatan.