Home Labaru Siyasar Kasar Gambia 

Siyasar Kasar Gambia 

11
0

A ranar 4 ga watan Disamba ‘Yan Gambia zasu yi zaben Shugaban Kasa . Hakan na zuwa ne kuma yayinda aka sake jinkirta fitarda rahoton hukumar tattara gaskiya game da zargin cin zarafin da aka aikata akan bil adama a lokacin mulkin Yahya Jammeh na shekaru 22.

Hukumar tace tana bukatar karin lokaci domin ta kammala aikinta. Mr Jammeh dake gudun hijira ya ki baiwa hukumar hadin-kai. Kuma a yanzu jam’iyyar Shugaba Barrow ta kulla kawance tare da jam’iyyar tsohon shugaba Jammeh, da kuma wasu jam’iyyu, gabanin zaben.

Shugaba Barrow ne dai ya kada Mr Jammeh a shekarar 2016, a wani zabe da ya tilasta masa barin mulki. Duka dai wannan ya sa ana kara fargabar cewa ba za a taba yin adalci ba, kamar yadda za ku gani a rahotan Thomas Naadi