Home Labaru Boko Haram Na Da Masana’antar Bom A Kaduna – Bincike

Boko Haram Na Da Masana’antar Bom A Kaduna – Bincike

22
0

Kungiyar Boko Haram ta sauya wa masanantar kera bama-bamanta zuwa wasu dazuka da ke sassan Jihar Kaduna.

Kafar yada labarai ta PRNigeria ta ce bangaren kungiyar Boko Haram  karkashin jagorancin Bakoura Buduma ne ya sauya wa masana’antun bom din kungiyar matsuguni.

PRNigeria ta ambato majiyoyin cikin gida na kungiyar na cewa an girke masana’antun bom din da kungiyar kera makamai ne a dazukan da ke yankunan Rijana, Igabi, da Chikun a Jihar Kaduna a matsayin maboya.

Majiyoyin sun kara da cewa hakan na faruwa ne a yayin da  shugabancin kungiyar ISIS ke neman hadewa da rassanta a yankin Yammacin Afirka, wato ISWAP.

Ana zargin hakan na da nasaba ne da kashe dimbin mayakan kungiyar da sojojin gwamnati suka yi a baya-bayan nan, a yankin Yammacin Afirka.

A ’yan makon jiya ne dai sojojin Najeriya suka sanar da kashe sabon shugaban kungiyar ISWAP, Malam Bako, watanni kadan bayan kashe shugabanta na farko, Abu Mus’aba Al-Barnawa.

Shi ma shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya mutu, kuma tum bayan mutuwar shugabannin nasu, suke fama da rikicin shugabanci, a yayin da sojoji ke ci gaba da yi musu luguden wuta.