Home Labaru Ba Za A Yi Zaɓe A Jihar Anambra Ba Sai An Saki...

Ba Za A Yi Zaɓe A Jihar Anambra Ba Sai An Saki Nnamdi Kanu

27
0

Kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra IPOB, ta gindaya sharadin cewa, matukar ba a saki Nnamdi Kanu ba za ta tsaida duk wata hada-hada a yankin kudu maso gabashin Nijeriya daga ranar 5 zuwa 10 ga watan Nuwamba na shekara ta 2021.

Tuni dai shugabannin ƙungiyar sun ba gwamnatin tarayya wa’adin mako ɗaya ta saki jagoran su Nnamdi Kanu, lamarin da ke nufin ba za ta bari a gudanar da zaɓen gwamnan Jihar Anambra da hukumar zaɓe za ta yi ranar 6 ga watan Nuwamba.

Kungiyar IPOB, ta ce ta yi amanna cewa ba za a yi wa Nnamdi Kanu adalci ba a shari’ar da ya ke fuskanta ta cin amana da neman raba ƙasa a gaban Babbar Kotun Tarayya ba.

Sai dai shugaban hukumar zabe ta kasa Farfesa Mahmud Yakubu ya ce sun shirya gudanar da zaɓen, ya na mai cewa sun farfaɗo daga hare-haren da aka kai a kan gine-ginen su.