Home Labaru Ilimi An Saki Sakamakon Jarabawar Kammala Sakandare Ta NECO

An Saki Sakamakon Jarabawar Kammala Sakandare Ta NECO

11
0

Hukumar shirya jarabawar kammala sakandare ta Nijeriya NECO, ta fitar da sakamakon jarabawar shekara ta 2021.

Shugaban hukumar Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi ya sanar da haka a helkwatar hukumar da ke Minna a jihar Neja.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Farfesan ya ce a cikin dalibai Miliyan 1 da dubu 233 da 631 da su ka yi rijistar jarabawar ta bana, mutane Miliyan 1 da dubu 226 da 796 su ka samu nasarar rubutawa, adadadin da ya  hada da Maza dubu 657 da 389 da kuma Mata dubu 576 da 242.

Farfesa Wushishi ya kara da cewa, daga cikin wadannan dalibai, mutane dubu 878 da 925 su ka samu nasarar samun akalla makin ‘C’ a darussa 5 da su ka hada da Turanci da Lissafi.

Ya ce an kama akalla mutane dubu 20 bisa laifin magudi da satar amsa a lokacin jarabawar, yayin da a jihohin Bauchi da Kaduna da Bayelsa an dakatar da makaranta daya kowannen su, yayin da aka dakatar da makarantu biyu a jihar Katsina na tsawon shekaru biyu bisa laifin taimaka wa dalibai wajen satar amsa.