Home Labaru An Bada Shawarar Sauke Sarakunan Da Ke Da Hannu A Rikicin Zamfara

An Bada Shawarar Sauke Sarakunan Da Ke Da Hannu A Rikicin Zamfara

221
0
Mohammed Bello Matawalle, Gwamnan Jihar Zamfara
Mohammed Bello Matawalle, Gwamnan Jihar Zamfara

Kwamitin da gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya kafa domin gano masu hannu a kashe-kashe da garkuwa da mutane a Jihar, ya mika rahoton sa, inda ya kama sojoji da sarakunan gargajiya da hannu wajen rura wutar rikicin.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne, shugaban kwamitin kuma tsohon shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya M.D Abubakar ya gabatar da sakamakon binciken kwamitin ga gwamnan jihar Bello Matawalle.

Rahoton ya cigaba da cewa, akwai sarakuna biyar da hakimai 33 da dagatai masu tarinn yawa, wadanda aka tabbatar su na da hannu a hare-haren da aka rika kaiwa a jihar Zamfara.

Kwamitin, ya kuma kama wasu jami’an soji 10 da laifi, da wasu jami’an ‘yan sanda, da jama’ar gari masu goyon bayan ‘yan bindigar da su ka kashe daruruwan jama’a. Da ya ke jawabi, Gwamna Matawalle ya ce zai yi amfani da duk abin da rahoton kwamitin ya bada shawara a yi, ba tare da shakka ko tsoron kowa ba, ya na mai cewa babu ruwan shi da kusanci da wani mai hannu a wannan rahoton da aka bada.