Home Home Ba A Sace Ko Kashe Ɗan Kasar Mu Ko Ɗaya Ba A...

Ba A Sace Ko Kashe Ɗan Kasar Mu Ko Ɗaya Ba A Harin ‘Yan Bindiga A Anambra Ba – Amurka

345
0

Mahukunta a kasar Amurka, sun ce maharan da ake zargin ‘yan kungiyar IPOB ne sun kai wa motocin ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya hari yayin wata ziyarar aiki da ta kai su jihar Anambra.

Rahotanni sun ce, ‘yan bindigar sun cinna wa motocin ma’aikatan wuta, sannan su ka yi awon gaba da wasu jami’an ‘yan sanda biyu da wasu ma’aikata, wadanda duk ‘yan Nijeriya ne baya ga wadanda su ka arce da su cikin daji.

Mahuntan kasar Amurka, sun ce babu wani dan kasar su da aka kashe ko aka sace a harin, sai dai su na tattaunawa da jami’an tsaron Nijeriya domin sanin ainihin abin da ya faru. Duk da cewa babu wata kungiya da ta fito ta ce ita ce ta aikata wannan mummunan lamarin, amma ana zargin kungiyar ma su fafutukar kafa kasar Biafra ne su ka kai harin.

Leave a Reply