Ministan Ilimi Adamu Adamu, ya zargi ‘yan Arewacin Nijeriya da zama musabbabin yaduwar jahilci a yankin.
Adamu Adamu, ya ce duk da cewa ‘yan Arewa su na bugun kirji da addinin Musulunci da ke karfafa neman ilimi, amma su su ke yi wa harkar neman ilimi manakisa.
Ya ce jami’o’i biyu na farko a duniya mata Musulmi ne su ka kafa su, amma wasu a yankin Arewa su na fakewa da addinin Musulunci su na hana mata fita neman ilimi.
Ministan ya bayyana haka ne, a wani taron kaddamar da manhajar karatun jami’o’i da wani littafi a kan sa da Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa NUC ta gudanar a Abuja.
Ya ce an kaddamar da sabuwar manhajar karatun jami’o’in ne domin tabbatar da ilimin jami’o’i a Nijeriya ya dace da zamani, sannan ya yi kira da a yi duk mai yiwuwa wajen sama masu wadatattun kayan aiki domin cimma wannan buri.