Home Home Majalisa Ta Amince Da Dokar Tsayawa Takarar Indifenda

Majalisa Ta Amince Da Dokar Tsayawa Takarar Indifenda

265
0

Majalisar Dattawa ta amince da dokar halasta tsayawa takarar zabe ba a karkashin kowace jam’iyya ba a Nijeriya.

Amincewar Majalisar da kudurin dai, zai ba daidaikun mutane masu cin gashin kan su damar tsayawa takarar kujerar shugaban kasa da gwamna da shugabancin kananan hukumomi ko wakilici a majalisar dokoki ba tare da jingina a wata jam’iyya ba.

Majalisar, ta kuma amince da kudurin dokar sanya Shugaban Majalisar Dattawa da na Majalisar Wakilai a cikin ‘yan Kwamitin Tsaro na Kasa.

Haka kuma, Majalisar ta umarci Akawun Majalisar Dokoki ta Kasa ya gabatar da kudurorin biyu da ta kammala karatu tare da amincewa da su ga Shugaba Muhammadu Buhari domin ya sanya hannu.

Dokokin biyu dais u na daga cikin sauye-sauyen da aka yi wa kundin tsarin mulki da aka aike wa Fadar Shugaban Kasa a karshen shekarar da ta gabata.

Leave a Reply