Home Labaru Ayyukan Raya Kasa: Shugaba Buhari Ya Sanya Wa Kasafin Shekara Ta 2019...

Ayyukan Raya Kasa: Shugaba Buhari Ya Sanya Wa Kasafin Shekara Ta 2019 Hannu

250
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sa hannu a kasafin shekara ta 2019.

An gudanar da bikin sanya hannun ne a ofishin Shugaban kasa da misalin karfe 11 na safiyar Litinin, 27 ga watan Mayu na shekara ta 2019.

Daga cikin mahalarta bikin rattaba hannun kuwa akwai shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara, da Shugaban kwamitin kasafi na majalisar dattawa Danjuma Goje, da Ministan kasafi da tsare-tsare Udoma Udo Udoma, da babban mai ba Shugaban kasa shawara a kan harkokin majalisar dattawa Ita Enang.

Sauran sun hada da ministar kudi Zainab Ahmed, da ministan yada labarai Lai Mohammed, da gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele, da shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa Abba Kyari, da kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha.