Home Labaru Yaki Da Rashawa: Majalisar Tarayya Na Yi Wa Dokar Da Ta Kafa...

Yaki Da Rashawa: Majalisar Tarayya Na Yi Wa Dokar Da Ta Kafa EFCC Kwaskwarima

353
0
Majalisa Za Ta Binciki Zargin Badakala Naira Biliyan 40 A Hukumr NCDC
Majalisa Za Ta Binciki Zargin Badakala Naira Biliyan 40 A Hukumr NCDC

Rahotanni na cewa, ‘yan majalisar tarayya za su yi wani yunkurin karshe da zai iya fatattakar shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu daga ofis ta hanyar yi wa dokar da ta kafa hukuma ta 2004 kwaswarima.

Tuni dai kudirin ya samu shiga majalisar wakilai, inda ake sa ran Sanatoci su kammala na su aikin a cikin wannan makon.

Idan dai kudirin ya samu karbuwa, zai kasance dole sai jami’in dan sandan da ya kai akalla Mataimakin shugaban ‘yan sanda na kasa ne zai iya rike hukumar maimakon matimakin kwamishina.

Majalisar dai ta yunkurin sauke Ibrahim Magu ne daga shugabancin hukumar EFCC, tare da maye gurbin sa da wani babban jami’in da ya kai akalla matakin AIG.

Haka kuma, ‘yan majalisar su na so shugaban hukumar EFCC ya kasance ya yi shekaru 15 zuwa 20 ya na aiki, ko kuma ya kasance ya na da ilmin shari’a.