Home Labaru Attajiran Najeriya Sun Yiwa Super Eagles Alkawarin Kudade

Attajiran Najeriya Sun Yiwa Super Eagles Alkawarin Kudade

992
0
Aliko Dangote (L) Da Femi Otedola (R)
Aliko Dangote (L) Da Femi Otedola (R)

Manyan Attajiran Najeriya biyu, Aliko Dangote da Femi Otedola, sun yiwa ‘yan wasan babbar kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles dake fafatawa a gasar cin kofin nahiyar Afirka a Masar alkawarin kudade idan sun samu nasara a sauran wasannin su biyu da suka rage, bayan nasarar da suka samu a wasan daf da na kusa da na karshe kan Afirka ta kudu.

Yayin ziyarar da suka kai wa kungiyar a masaukin su dake Birnin Alkahahira, Aliko Dangote, ya yi alkawarin biyan Dala dubu 50, kan kowanne kwallo guda da kungiyar ta jefa a wasannin da za suyi nan gaba, yayin da Femi Otedola ya yi alkawarin biyan Dala dubu 25,  kan kowanne kwallo guda.

Karanta labaru Masu Alaka: Obi Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ya Kaurace Wa Super Eagles

Kafin wannan alkawarin, wani attajirin mai harkar mai, Captain Hosea Wells Okunbo, ya yiwa kowanne dan wasa guda alkawarin Dala dubu 20, idan sun doke kamaru kuma ya biya su bayan nasara da suka samu, kana shima Gwamnan Lagos Babajide Sanwo-Olu, ya ba kowanne dan wasa Dala dubu 5, saboda gagarumar nasara da suka samu akan Kamaru.

Ita ma kamfanin man AITEO dake hadin gwuiwa da Hukumar kwallon kafar Najeriya ta biya Dala dubu 25, akan kowanne kwallo guda da Najeriya ta jefa a wasan Kamaru.

Leave a Reply