Home Labaru Harin Al Shebab: Mutane Da Dama Ne Suka Mutu

Harin Al Shebab: Mutane Da Dama Ne Suka Mutu

290
0

‘Yan kungiyar Al’Shebab dauke da manyan makamai sun yi garkuwa da wasu mutane a wani gidan Otel dake Kismayo.

Jami’an tsaro sun share daren jiya suna kokarin kubutar da mutanen dake cikin wanan Otel.

Majiyar tsaro ta Somalia ta bayyana mutuwar mutut 12, daga cikin mutanen da aka rasa kuma akwai wani Minista da wani dan Majalisa, yayinda wasu 30 suka samu raunuka.

Karanta Labaru Masu Alaka: Amurka Ta Gargadi Amurkawa Akan Zuwa Najeriya

Jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da bincike domin tanttance masu bayar da goyan baya ga ‘yan kungiyar Al’Shebab a wadanan hare-hare dake hadasa mutuwar jama’a da dama a kasar ta Somalia.