Home Labarai INEC Ta Fitar Da Sunayen ‘Yan Takarar Gwamna Da Na Majalisun Jihohi

INEC Ta Fitar Da Sunayen ‘Yan Takarar Gwamna Da Na Majalisun Jihohi

393
0

Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta fitar da jerin sunayen ‘yan takarar gwamna da na majalisun Jihohi gabanin kaddamar da yakin neman zaben su a hukumance ranar 12 ga watan Oktoba.

INEC ta ce ta sa ido a kan dukkan zabubbukan kuma ta bar gurbin sunayen ‘yan takarar da ke shari’ar sahihin dan takara a kotu.

Jami’a a sashen yada labaru na hukumar Zainab Aminu, ta ce hukumar a shirye ta ke ta cike guraben da duk wadanda kotu ta yanke hukuncin su ne sahihan ‘yan takara.

Za a dai gudanar da zaben gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi ne a ranar 11 ga watan Maris na shekara ta 2023.

Leave a Reply