Home Labaru Atiku Bai Cika Sharudan Lashe Zabe Ba —Inec

Atiku Bai Cika Sharudan Lashe Zabe Ba —Inec

1
0

Hukumar Zabe mai zaman kan ta ta Kasa INEC, ta ce dan
takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar bai
cika sharuddan da kundin tsarin mulkin Nijeriya ya gindaya
ba na lashe zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.

Don haka hukumar zaben ta bukaci kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta yi watsi da karar da Atiku da jam’iyyar sa su ka shigar su na kalubalantar sakamakon zaben.

Hukumar zaben ta bayyana wa kotun cewa, Atiku ya gaza samun akalla kashi daya bisa hudu na kuri’un da aka kada ko akalla kashi biyu bisa uku na jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, don haka babu yadda za a ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara.

Ta ce an gudanar da zaben ne bisa ka’ida da dokar zabe ta shekara ta 2022, kuma dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC Bola Tinubu ne ya lashe zaben da kuri’u miliyan 8 da dubu 794 da 726.

Atiku Abubakar da Bola Tinubu dai sun lashe jihohi 12 kowanen su, yayin da Peter Obi ya lashe jihohi 11 da birnin tarayya Abuja.