Magoya bayan Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar
Adamawa, sun shirya gudanar da zanga-zanga a Helkwatar
Hukumar Zabe ta Kasa reshen jihar.
Shugaban kungiyar Abdurrahman Bobbo ya bayyana haka, yayin gangamin goyon bayan Fintiri da wasu kungiyoyi 75 su ka shirya a Yola, inda ya ce ‘yan jihar za su yi da gaske wajen kare kuri’un su gare Fintiri duk kuwa da irin adawar da ya ke fuskanta.
Ya ce ‘yan Adamawa ba za su taba bari a sace kuri’ar da su ka jefa wa Fintiri ba, don haka za su mamaye helkwatar hukumar zabe daga ranar Asabar har zuwa lokacin da za a ba
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri takardar shaidar lashe zaben.
Yayin da ya ke nanata kudurin su na tabbatar da an yi abin da
ya dace, Bobboi ya ce kishin jama’a zai yi galaba a kan
muradun wadanda su ka samu umarni daga sama na lalata
tsarin zabe da ‘yancin jama’a.
Bobboi ya kara da cewa, jihar Adamawa ta PDP ce, shi ya sa
ta doke APC a zabubbukan da aka yi kuma a bayyane ya ke
cewa za ta lashe wanda ke tafe.
You must log in to post a comment.