Home Home ASUP Ta Yi Fatali Da Umarnin Gwamnati Kan Haramta Wa Makarantun Kimiyya...

ASUP Ta Yi Fatali Da Umarnin Gwamnati Kan Haramta Wa Makarantun Kimiyya Bada Digiri

101
0
Ƙungiyar Malaman Makarantun Kimiyya ta Ƙasa ASUP, ta yi watsi da umarnin da Gwamnatin Tarayya ta ba makarantun su daina bada takardar shaidar digiri.

Ƙungiyar Malaman Makarantun Kimiyya ta Ƙasa ASUP, ta yi watsi da umarnin da Gwamnatin Tarayya ta ba makarantun su daina bada takardar shaidar digiri.

A makon da ya gabata ne, Gwamnatin tarayya ta hannun Hukumar Kula Da Ilimin Fasaha ta Ƙasa NBTE, ta haramta wa makarantun kimiyyar bada takardar shaidar digiri.

Shugaban kungiyar ASUP na ƙasa Anderson Ezeibe, ya ce makarantun su na da ƙarfin da ake buƙata na kayan aiki da manhajojin da ake buƙata domin bada digiri.

Ezeibe, ya ce ya yi mamakin dalilin da ya sa har yanzu gwamnatin tarayya ba ta bada irin wannan umarnin ga jami’o’in da ke bada takardar difloma da sauran takardun digiri ba, ya na mai bayyana umarnin a matsayin wariya ga masanan kimiyyar ƙere-ƙere ta Nijeriya.

Leave a Reply