Home Labaru Kiwon Lafiya Asibitin Aminu Kano Ya Dakatar Da Zuwa Dubiyar Marasa Lafiya.

Asibitin Aminu Kano Ya Dakatar Da Zuwa Dubiyar Marasa Lafiya.

395
0
Asibitin Aminu Kano Ya Dakatar Da Zuwa Dubiyar Marasa Lafiya.
Asibitin Aminu Kano Ya Dakatar Da Zuwa Dubiyar Marasa Lafiya.

Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) ya dakatar da zuwa dubiyar marasa lafiya da aka kwantar a asibitin

Asibitin ya ce daga yanzu mutum daya kadai za a bari daga ‘yan uwan mara lafiya ya shiga harabar asibitin, idan har akwai bukatar hakan.

Shugaban asibitin, Farfesa Abdurrahman Abba Sheshe, ya kuma bukaci masu zuwa ganin likita da su daina zuwa da ‘yan rakiya.

Sanarwar da Asibitin ta fitar ta ce hakan na daga matakan da ta dauka na rage taruwar jama’a, da zummar dakile yaduwar cutar coronavirus a tsakanin mutane.

Cutar coronavirus na ci gaba da yaduwa a duniya, lamarin da ya tilasta sanya dokar hana fita da taron jama’a a wasu kasashe.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce annobar cutar mai yaduwa, ta yi ajalin dubban mutane, tare da kwantar da wasu sama da 300,000.

Bakuwar cutar ta coronavirus wadda ta fara bulla a watan Disamban 2019, na ci gaba da tayar da hankulan hukumomin duniya da ke ta kokarin samo maganin cutar.

Leave a Reply