Home Labaru Kiwon Lafiya Masu Covid-19 A Najeriya Sun Karu Zuwa 40 – NCDC.

Masu Covid-19 A Najeriya Sun Karu Zuwa 40 – NCDC.

879
0
Masu Covid-19 A Najeriya Sun Karu Zuwa 40 - NCDC.
Masu Covid-19 A Najeriya Sun Karu Zuwa 40 - NCDC.

 Mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya sun karu zuwa mutum 40.

Hukumar Hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya NCDC, ta ce adadin ya karu ne bayan samun karin mutum 4 da suka kamu da cutar a ranar Litinin.

NCDC ta ce uku daga cikin sabbin masu cutar an same su ne a jihar Legas, 1 kuma a Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Zuwa yanzu an samu bullar cutar a jihohi biyar a Najeriya.

Mutum 27 na dauke da cutar a jihar Legas, sai kuma mutum 7 a Abuja.

Jihar Ogun na da mutum 2 sai kuma jihohin Edo, Ekiti da kuma Oyo da aka samu mutum daya a kowannensu.

 NCDC ta ce daga cikin mutum 40 da suka kamu da coronavirus a Najeriya, an sallami mutum 2 daga asibiti, 37 na karbar magani, sai kuma mutum 1 da ya rasu.