Majalisar Dattata tabbatar da Manjo Janar Paul Tarfa mai ritaya da sauran zababbun ‘yan kwamitin habaka ci-gaban Arewa maso Gabas da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada.
Rahotanni sun bayyana cewa, Manjo Janar Tarfa zai jagoranci kwamitin tabbatar da habaka ci-gaban yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya.
Majalisar dattawa ta yi na’am da nadin mukaman shugaban Buhari, yayin shugaban kwamitin bincike a kan nadin mukamai na ayyukan musaman Sanata Abdul’aziz Nyako ya gabatar da sakamakon sa.
You must log in to post a comment.