Home Labaru Ta’addanci: ‘Yan Ta’adda Da Jami’an Sa-Kai Sun Yi Ba-Ta-Kashi A Jihar Katsina

Ta’addanci: ‘Yan Ta’adda Da Jami’an Sa-Kai Sun Yi Ba-Ta-Kashi A Jihar Katsina

1045
0

Rahotanni na cewa, akalla mutane 14 aka kashe a karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina, sakamakon wata arangama tsakanin ‘yan ta’adda da jami’an sa-kai da aka fi sani da ‘yan bijilanti.

Lamarin dai, ya faru ne a garin Tsamiyar Jino da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina, kamar yadda mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina SP Gambo Isah ya tabbatar.

SP Isah, ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da ‘yan sintirin su ka shirya kaddamar da kai hari a maboyar ‘yan ta’addan da ke cikin daji, inda su ka kashe bakwai daga cikin su, yayin da ‘yan ta’addar su ma su ka kashe bakwai daga cikin ‘yan sintirin.

Ya ce Tuni shugaban ‘yan sanda na yankin ya isa inda lamarin ya faru, kuma an kwantar da tarzoma, sannan an shawarci jami’an sa-kan su daina daukar hukunci a hannun su, su kasance masu neman hadin gwiwar sauran jami’an tsaro da doka ta yarda da su, musamman su taimaka wajen bada bayanan da za su kawo nasarar dakile ta’addanci.