Rahotanni na cewa, yanzu haka an janye rundunar sojojin Nijeriya daga garin Jakana da ke karamar hukumar Konduga ta jihar Borno, bayan an kwashe al’ummar garin zuwa birnin Maiduguri.
A baya dai rahotanni sun ce, rundunar sojin sama ta Operation Lafiya Dole, ta lalata wata mafakar ‘yan ta’addan kungiyar ISWAP, tare da kashe mayakan kungiyar da dama a garin Tumbun Zarami da ke gabashin jihar Borno.
Yayin gudanar da wani atisaye a sararin samaniya, rundunar sojin ta gano wata mafaka da mayakan ISWAP masu yawa ke fakewa ta hanyar amfani da na’urorin musamman a jirgin su na yaki.
Bayan gano sansanin ne, rundunar ta aika wasu jiragen ta biyu na musamman da suka yi kasa-kasa da sansanin ta hanyar yi masu ruwan boma-bomai da luguden wuta.
Lamarin dai, ya yi sanadiyar mutuwar mayakan kungiyar da dama, kamar yadda daraktan yada labarai da hulda da jama’a na rundunar soji sama Ibikunle Daramola ya sanar.