Jam’iyyar APC a jihar Kano, ta yi Allah wadai da rushe-
rushen da gwanmnatin Abba Kabir Yusuf ta ke yi, lamarin da
ta bayyana a matsayin farmaki a kan dukiyoyin al’umma.
A cikin wata sanarwa da muƙaddashin shugaban jam’iyyar na jihar Kano Shehu Maigari ya raba wa manema labarai, APC ta ce a yau Kano ta kasance abin tausayi saboda halin da jam’iyyar NNPP ta jefa ta a ciki, inda ta zargi NNPP da gwamnatin Abba Gida-Gida da jefa ‘yan kasuwa cikin mawuyacin hali.
Ta ce matakin da NNPP ta ɗauka na rusa wasu wuraren kasuwanci a jihar ya sa wasu matasa sun zama ɓarayi saboda su na yawo da makamai tare da fasa shagunan mutane domin satar kaya.
A karshe ta yi kira ga iyayen yara, musamman matasan da ta ce gwamnatin NNPP ta na amfani da su wajen ɓarnata kayan al’umma su ja kunnen ‘ya’yan su.














































