Home Labaru Obi Ya Gabatar Wa Kotu Da Sakamakon Zaɓen Jihohi Bakwai,

Obi Ya Gabatar Wa Kotu Da Sakamakon Zaɓen Jihohi Bakwai,

340
0

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Peter Obi, ya
gabatar wa Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa
sakamakon zaɓe daga jihohi bakwai.

Peter Obi, wanda aka bayyana a matsayin na uku, ya na iƙirarin cewa shi ne ya yi nasara a zaɓen da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu na shekara ta 2023.

Atiku Abubakar da Peter Obi dai sun yi zargin cewa an tafka maguɗi da ƙin bin ƙa’idojin zaɓe, wadanda su ka haɗa da ba Tinubu fifiko domin ya tsere wa sauran ‘yan takara a zaɓen da aka gudanar.

A na shi bangare, Dakta Rabi’u Kwankwaso na jam’iyyar NNPP da ya zo na huɗu, ya ce shi ne ma ya fi sauran ‘yan takara cancantar ya kai ƙara, amma ya haƙura saboda ba ya son ɓata lokaci.

Leave a Reply