Jam’iyyar APC reshen Jihar Adamawa, ta kori ‘yan kwamitin zartarwar ta 25 saboda rawar da su ka taka wajen sanar da dakatar da Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha daga jam’iyyar.
Shugaban jam’iyyar na mazabar da Boss Mustapha ya fito ne ya sanar da dakatar da shi a makon da ya gabata, bisa zargin shi da yi wa jam’iyyar kafar ungulu a zabubbukan da su ka gabata.
Sai dai a makon da ya gabata, mazabar da Sakataren Gwamnatin Tarayya ya kada kuri’ar sa ta Gwadabwa da ke Karamar Hukumar Yola ta Arewa ta yi fatali da dakatarwar da kuma zarge-zargen da aka yi masa.
Sakataren jam’iyyar APC na Jihar Adamawa Dakta Raymond Chidama, ya ce an dakatar da mutanen da abin ya shafa ne har zuwa wani lokaci nan gaba, sannan an umarci su mika kadarorin jam’iyyar ga Shugaban Karamar Hukumar Yola ta Arewa cikin gaugawa.
You must log in to post a comment.