Home Home Abin Da Ya Sa Muka Dakatar Da Iyorchia Ayu – PDP

Abin Da Ya Sa Muka Dakatar Da Iyorchia Ayu – PDP

99
0

Jam’iyyar PDP ta ce ta dakatar da shugaban ta na ƙasa Iyorchia Ayu ne bisa zargin shi da wasu ayyukan cin amanar jam’iyyar.

Shugabannin jam’iyyar na matakin gundumar sa da ke ƙaramar hukumar Gboko ta jihar Benue ne su ka ɗauki matakin, inda su ka ce sun dakatar da shi ne bayan kaɗa ƙuri’ar rashin ƙwarin gwiwa a kan ayyukan sa.

Lokacin da ya karanta matsayar da shugabannin su ka cimmawa, sakataren jam’iyyar na gundumar Igyorov, Vanger Dooyum, ya ce zagon-ƙasan da Ayu da na kusa da shi su ka yi wa PDP ne ya janyo mata shan kaye a gundumar da ma jihar baki ɗaya a zaɓen gwamna.

Sun kuma zargi Ayu da rashin biyan kuɗaɗen da ake karɓa na shekara-shekara daga ‘yan jam’iyyar, kamar yadda dokokin ta su ka tanada.

Leave a Reply