Home Labaru Samar Da Tsaro: Ya Kamata ‘Yan Najeriya Su Gode Wa Buhari– Adesina

Samar Da Tsaro: Ya Kamata ‘Yan Najeriya Su Gode Wa Buhari– Adesina

105
0

Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai Femi Adesina, ya ce kamata ya yi ‘yan Najeriya su gode wa shugaba Muhammadu Buhari, saboda kokarin da ya ke na yaki da rashin tsaro.

Femi Adesina, ya fadi haka ne yayin  da yake amsa tambayoyi a wani shirin siyasa na gidan talabijin na Channels.

Adesina ya ce shugaba Buhari, yana kokari wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar Najeriya, duk da cewa a bayyane ya ke akwai matsalolin tsaro a sassa da dama musamman ma yankin arewa.

Ya ce amma ba Najeriya ce kawai ke fuskantar matsalolin tsaro ba, kasashe da dama a duniya na fama da kalubalen tsaron, dan haka abinda ya kamata ‘yan Najeriya su yi shi ne taya shugaban kasa addu’a ba suka mara ma’ana ba.