Home Labaru Kiwon Lafiya Annobar Corona: Ka Da Wanda Ya Sake Zuwa Ofishin ‘Yan Sanda-Muhammad Adamu

Annobar Corona: Ka Da Wanda Ya Sake Zuwa Ofishin ‘Yan Sanda-Muhammad Adamu

242
0
Annobar Corona: Ka Da Wanda Ya Sake Zuwa Ofishin ‘Yan Sanda-Muhammad Adamu
Annobar Corona: Ka Da Wanda Ya Sake Zuwa Ofishin ‘Yan Sanda-Muhammad Adamu

Shugaban ‘yan sandan Nujeriya Muhammad Adamu, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su dakatar da kai ziyarce-ziyarce zuwa ofisoshin ‘yan sanda da ke fadin Nijeriya domin gudun yaduwar cutar Corona.

Muhammad Adamu ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya su daina zuwa caji ofis a wannan lokaci da annobar Corona ta yi kamari, sakamakon yadda  adadin masu dauke da cutar su ka kai 30 a Nijeriya.

Adamu ya bayyana haka ne ta bakin kakakin rundunar DCP Frank Mba, inda ya shawarci ‘yan Nijeriya su kasance masu biyayya ga tsare -saren da aka gindaya na kauce wa yada cutar a Nijeriya.

Haka kuma, Muhammad Adamu ya gargadi jami’an ‘yan sanda su guji kama mutanen da basu ji ba basu gani ba, musamman ba tare da wata kwakkwaran hujja ba.

Adamu  ya kara da cewa, dole ne a rage kama mutane, sai dai wadanda suka aikata munana laifuka kamar su fashi da makami da ta’addanci da kisan kai da kuma sauran laifukan da doka ta haramta bada beli a kan wanda ya aikata su.

A  karshe Muhammad Adamu ya bada umarnin rufe dukkanin makarantun ‘yan sanda dake fadin Nijeriya, tare da bukatar ‘yan sanda su tabbata sun dabbaka umarnin gwamnati na hana taruwar mutane da yawa a waje guda.