Hukumar Jami’ar Bayero da ke jihar Kano ta karyata batun cewa an samu bullar cutar corona a jami’ar.
Idan dai ba a manta ba, a ranar Lahadi da ta gabata ne wasu suka fara yada farfagantar cewa, ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta tabbatar da samun wasu dalibai biyu da suka kamu da cutar corona a jami’ar Bayero.
Sai dai, shugaban Jami’ar Farfesa Muhammad Yahuza ya danganta labara a matsayin mara tushe balle makama, tare da cewa babu dalibai a dakunan kwanan jami’ar.
Farfesa Yahuza ya ce, tuni jami’ar ta bada hutun mako guda, sai kuma ga batun yajin aikin gargadi na makonni biyu da malaman jami’o’i suka shiga.
A karshe Yahuza ya yi Allah-wadai da wadanda suka kirkiri wannan labaran na karya, kana kuma ya yi kira ga masu yadawa irin wannan labaran da su guji yin haka.
You must log in to post a comment.