Home Coronavirus Annoba:Hukumar NCDC Tace Ƙarin Mutum 562 Sun Kamu Da COVID-19

Annoba:Hukumar NCDC Tace Ƙarin Mutum 562 Sun Kamu Da COVID-19

215
0
Cutar Corona: Hukumar NCDC Ta Tsaurara Matakai A Tashoshin Nijeriya
Cutar Corona: Hukumar NCDC Ta Tsaurara Matakai A Tashoshin Nijeriya

Alƙaluman da hukumar dakile cutuka masu yaɗuwa ta fitar sun nuna cewa covid-19 ta sake kashe mutum 12 a faɗin Najeriya.

Ƙididdigar da hukumar ke fitarwa a kullum ya nuna cikin mako ɗaya cutar ta kashe mutum kusan 60 daga 13 ga watan Yuli zuwa 20 ga wata.

Alƙalumman sun kuma nuna yanzu cutar ta yi ajalin mutum 801, ƙasa da wata biyar bayan ɓullarta.

NCDC ta kuma nuna cewa masu covid-19, 228 ne suka warke har kuma an sallame su ranar Litinin don komawa gida cikin iyalansu.

Hakan ya nuna har yanzu akwai masu cutar 21,892 da ke kwance suna jinya a cibiyoyin kwantar da masu cutar na faɗin Najeriya.

Haka zalika Mutum 562 sun kamu da cutar cikin sa’a 24, wanda hakan da ya sa yawan mutanen da cutar ta harba a ƙasar ya kai 37,225.