Home Labaru Kiwon Lafiya Annoba: Kyanda Ta Kashe Yara 17, Wasu Dubu 10 Sun Kamu A...

Annoba: Kyanda Ta Kashe Yara 17, Wasu Dubu 10 Sun Kamu A Borno

427
0

Yara kanana 17 masu watanni 6 zuwa 5 ne, aka tabbatar da cewa sun mutu, sannan kuma wasu  dubu 10  suka kamu da cutar  kyanda a jihar Borno.

Darakta yaki da yaduwar cututtuka na ma’aikatar kula da lafiya a matakin farko a jihar Borno, Babagana Abiso, ne ya tabbatar da haka a lokacin da yake zantawa da manema a Maiduguri na jihar Borno.

Abiso, ya ce gwamnati za ta yi iya bakin kokarinta wajen daukar matakin gudanar da rigakafi ga kananan yara ‘yan kimanin watanni 6 zuwa shekaru 6 a kananan hukumomi 15 domin shawo kan matsalar a jihar Borno.

Ya ce da farko an sami karancin kayayyakin aikin rigakafin, lamarin da ya janyo tsaiku a wasu yankunan da lamarin ya safa.

Daraktan ya ce sun gano gundumomi 8 wadanda matsalar tafi tsanani, sauran kananan hukumomi 12 da suka rage, kuma a kowanne lokaci za su sam rigakafin daga gwamnati.

Leave a Reply