Mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya koka a game da yadda yunwa da talauci suka dabaibaye Arewacin Najeriya.
Sarkin na Kano ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tsokaci kan wata takarda da tsohon shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya A.B Mahmood ya gabatar a wajen taron tunawa da marigayi Malam Aminu Kano wanda ya rasu shekaru 36 a gidan Mambayya dake Kano.
Sanusi na biyu, ya ce duk da yunkurin dabbakka shari’a a wasu jihohin Arewa, sai dai arewacin Najeriya na cikin wani halin matsi na tattalin arziki.
Sarkin ya bayyana cewa barawon gwamnati ya na yi wa jama’a illar da ta ribanya ta barawon akuya, domin haka akwai bukatar a sake duba lamarin shari’a.
Sarkin ya ce idan ba a sake duba dokokin aure da zaman iyali da sha’anin saki ba, dole arewa za ta ci gaba da ciran tuta wajen ta’addanci da shaye-shayen kwayoyi da garkuwa da mutane da matsalar Almajiranci da bangar siyasa. Sarkin Muhammadu Sanusi II, ya tabbatar da cewar nan da shekaru 20 zuwa 30 masu zuwa, arewa za ta yi fama da rikicin da ya fi na yau saboda ganin yadda ake da Almajirai miliyan 3 na gara-ramba a jihar Kano, wanda a cikin su babu wanda zai iya zama likita ko alkali a nan gaba.
You must log in to post a comment.