Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC da kuma hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, sun bayyana damuwar su dangane da yadda kashi 70 cikin 100 na magungunan da ke yawo a kasuwannin Nijeriya Jabu ne.
Mataimakin kwamandan hukumar NDLEA a jihar Anambra, Mista Adewumi Alfred, ya bayyana haka, inda ta ce yaduwa tare da shan miyagun kwayoyi na karuwa a Nijeriya, saboda a wani bincike na baya-bayannan, ya nuna cewar kashi 70 cikin dari na magungunan dake Najeriya jabu ne.
Hukumomin sun kara da tabbatar da cewa, kusan dukkanin manyan laifukan da ake aikatawa da bullar wasu cututtuka a tsakanin al’umma na da nasaba da sayarwa tare da shan irin wadannan magungunan barkatai.Daga karshen hukumomin na NAFDAC da kuma NDLEA, sun ce samar da magungunan ba bisa ka’ida ba, tare da safarar su zuwa Nijeriya, na daga cikin abubuwan da ke haifar da yawaitar mutuwar kananan yara da bullar cututtuka da sa fargaba a zukatan ‘yan Najeriya dangane da sha’anin kula da lafiya.