Home Labaru Kiwon Lafiya Annoba: Cutar Kwalara Ta Kashe Mutum 479 A Jihohi 18

Annoba: Cutar Kwalara Ta Kashe Mutum 479 A Jihohi 18

66
0

Hukumar dakile bazuwar cututtuka ta kasa wato NCDC ta bayyana cewa kawo yanzu  mutum 19,305  ne suka kamu da cutar kwalara a jihohin 18 da Birnin Tarayya.

Hukumar ta NCDC ta ce daga farkon wannan shekara zuwa ranar 11 ga Yulin 2021, mutum 19,305 ne suka kamu da cutar, daga cikinsu 479 sun rasu a jihohi 18 da Birnin Tarayya.

Kashi 11 cikin 100 da suka kamu da cutar kananan yara ne masu shekaru biyar zuwa 14. Kashi 52 cikin 100 na mutanen maza ne, sai mata kashi 48 cikin 100,” inji rahoton.

NCDC ta kara da cewa an samu karuwar masu kamuwa da cutar ta kwalara a jihohi hudu da suka hada da Kano da Bauchi da Jigawa da kuma Kwara.

Alkaluman da ta fitar sun nuna daga ranar 5 zuwa 11 ga watan Yuli mutum 31 ne cutar kwalara ta kashe a Najeriya.

Jihoin da aka samu bullarta su ne Kano da Kaduna da Zamfara da Gombe, da Bauchi da Jigawa da Nasarawa da Yobe da Binuwai.

Sauran su ne Kebbi da Kwara da Filato da Neja da Kogi da Delta Kuros Riba da Bayelsa da kuma Abuja.

Cutar kwalara tana iya kisa kuma an fi kamuwa da ita ne daga amfani da gurbataccen ruwa.