Home Labaru Zaman Lafiya: Shugaban Ivory Coast Ya Yi Sulhu Da Laurent Gbagbo

Zaman Lafiya: Shugaban Ivory Coast Ya Yi Sulhu Da Laurent Gbagbo

32
0

Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara da babban abokin hamayyarsa Laurent Gbagbo sun rungumi juna a haduwarsu ta farko tun bayan yaƙin basasar ƙasar shekaru goma da suka gabata.

Yaƙin ya faru ne bayan da Mista Gbagbo ya ƙi amincewa da kayen da ya sha a zaɓen kuma mutum 3,000 suka rasa rayukansu.

Mista Gbagbo,  ya koma Ivory Coast a watan jiya bayan da kotun hukunta manyan laifuka ta ICC ta wanke shi kan tuhume-tuhumen da ake masa na cin zarafin bil Adama

Mutanen biyu sun jima suna neman shiri da juna.

Mista Ouattara ya yi wa Mista Gbagbo maraba a fadar shugaban ƙasa a Abidjan, babban birnin ƙasar ranar Talata.

Wasu na ganin wannan ganawa a matsayin wata alama ta samar da masalaha a ƙasar amma kakakin Mista Gbagbo Justin Katinan Kone ya bayyana cewa “kada mutane su fiye damuwa da abin da zai faru”.

An kama Mista Gbagbo ne a fadar shugaban ƙasa a watan Afrilun 2011 sannan aka kai shi kotun ICC da ke The Hague. Bayan da kotun ta wanke shi ne ya zauna a Brussels kafin Mista Outtara ya gayyace shi ya dawo ƙasar Ivory Coast.