Home Coronavirus Annoba: Corona Ta Sake Kashe Mutum 4 A Najeriya

Annoba: Corona Ta Sake Kashe Mutum 4 A Najeriya

40
0
Chikwe-Ihekweazu-NCDC

Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 584 ne suka kamu da cutar korona a faɗin Najeriya a ranar Litinin.

Kuma alƙalumman sun nuna cewa cutar ta sake kashe mutum huɗu a ƙasar cikin sa’a 24.

Hukumar ta ce akasarin waɗanda suka kamu a jihar Legas suke, inda aka samu karin mutum 201 da suka kamu, yayin da a jihar Rivers aka samu mutane 149 da gwajin da aka yi musu ya tabbatar da cewa sun kamu da cutar.

A Abuja babban birnin Tarayya ƙarin mutum 82 suka kamu da cutar.

An kuma samu ƙaruwar yaɗuwar cutar a jihohin Kano da Kaduna da Sokoto, kamar yadda alƙalumman suka nuna.

Wadanda suka kamu 183,087 wadanda suka mutu 2,223 wadanda aka sallama 167,310.