Home Coronavirus Annoba: Ƙarin Mutum 497 Sun Kamu Da Cutar Korona A Najeriya

Annoba: Ƙarin Mutum 497 Sun Kamu Da Cutar Korona A Najeriya

94
0

Alkaluman da hukumar daƙile cututtuka masu yaduwa ta Najeriya ta fitar ranar Juma’a sun nuna cewa wasu ƙarin mutum 497 sun kamu da cutar korona jiya Asabar.

Ya zuwa yanzu adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 173,908, kodayake an sallami 164,994 da aka tabbatar sun warke garau. Sai kuma mutum 2,149 da suka rasa rayukansu.

A baya-bayan nan ne aka samu ɓullar sabon nau’in cutar korona da ake kira Delta a kasar wanda masana ke cewa yana da saurin yaɗuwa matuƙa.

Ga jerin jihohin da aka samu masu ɗauke da cutar ranarJuma’a.

Legas-211, Akwa Ibom-80, Kwara-73, Osun-29, Oyo-17, Rivers-17, Cross River-15, Edo-14, Anambra-9, Ogun-8, Ekiti-6, Bayelsa-4, Abuja-4, Plateau-4, Bauchi-2, Nasarawa-2, Kaduna-1, Jigawa-1