Home Coronavirus Coronavirus A Najeriya: Ana Duba Yiwuwar Sake Kafa Dokar Kulle A Wasu...

Coronavirus A Najeriya: Ana Duba Yiwuwar Sake Kafa Dokar Kulle A Wasu Yankunan

215
0

Mahukunta a Najeriya sun yi gargadin cewa kasar ta fara shiga mataki na uku na annobar korona a kwanakin baya baya nan, har ma an sami kimanin mutum goma da suka kamu da sabon nau’in annobar mai suna delta.

Sai dai sun ce ana ci gaba da bin dukkan matakan da suka kamata don ganin an dakile yaduwarta.

Wani jami’i a Kwamitin Shugaban Najeriya da ke yaki da annobar korona, Dakta Muktar Muhammed, ya shaida wa BBC Hausa cewa yanzu haka mahukunta na duba yiwuwar sake kafa dokar kulle a wasu yankuna da cutar ta fi yaɗuwa.

Ya kara da cewa sai dai a wanan karon ba za ta kasance ta bai-ɗaya ba, a maimakon hakan za a yi duba da inda aka fi samun yaɗuwar cutar ne a jihohi da ma tarayya baki ɗaya.

A cewarsa, “A gaskiya a kwanakin baya mun ga cewa annobar ta ja baya, domin ba a samun masu kamuwa da cutar sosai, amma yanzu yawan ya karu, saboda mutane sun daina daukar matakan kariya, don haka ba abin mamaki ba ne idan yawan ya karu ayanzu.”

Ya ce zuwa yanzu an gano mutanen da suka kamu da cutar nau’in Delta akalla goma sha wani abu, “don haka lallai akwai wannan nau’u a Najeriya kuma yana dada karuwa, muna ma zargin cewa za a iya danganta karuwar masu kamuwa da cutar da shi wannan nau’i a yanzu haka.

Leave a Reply