Home Labaru Ana Jimamin Shekara 12 Da Kisan Sheikh Jafar

Ana Jimamin Shekara 12 Da Kisan Sheikh Jafar

1171
0

A ranar Asabar dinnan ne fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Najeriya, Sheikh Jafar Mahmud Adam, ya cika shekara 12 da rasuwa.
Wasu ‘yan ta’adda ne dai suka harbe malamin yayin da yake Sallar Asuba a ranar 13 ga watan Afrilun shekarar 2007 a Kano, wato jajiberin zaben gwamnoni da aka yi a shekarar.
Marigayin yana daya daga cikin manyan malaman addini a bangaren mabiya Sunnah da ke da dimbin magoya baya a Najeriya.
Kuma bayan wallafa hotonsa a shafukan sada zumunta a ranar da ya cika shekara 12 da rasuwa an samu dubban sakonnin dake nuna alhini game da mutuwar sa.
Duk da cewa har yanzu jama’a na ci gaba da bayyana mutuwar sa a matsayin wani babban rashi, amma kuma har yanzu babu wani da aka kama da laifin kisan malamin.